{"id":3332,"date":"2026-08-28T13:30:04","date_gmt":"2026-08-28T13:30:04","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=3332"},"modified":"2026-08-28T13:30:04","modified_gmt":"2026-08-28T13:30:04","slug":"najeriya-ta-fara-gyaran-cibiyoyin-horar-da-yan-sanda-guda-13","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/08\/28\/najeriya-ta-fara-gyaran-cibiyoyin-horar-da-yan-sanda-guda-13\/","title":{"rendered":"Najeriya Ta Fara Gyaran Cibiyoyin Horar da &#8216;Yan Sanda Guda 13"},"content":{"rendered":"<p><strong>Gwamnatin Najeriya ta bayar da kwangilolin gyaran cibiyoyin horar da &#8216;yan sanda guda 13 a sassa daban-daban na kasar.<\/strong><\/p>\n<p>An tsara shirin gyaran wanda zai dauki tsawon makonni uku domin shirya wadannan cibiyoyi don fara shirye-shiryen horarwa na rundunar &#8216;yan sandan Najeriya.<\/p>\n<p><img decoding=\"async\" src=\"https:\/\/von.gov.ng\/wp-content\/uploads\/2026\/08\/IMG-20260827-WA0120.jpg\" \/><\/p>\n<p>An gabatar da wannan sabon bayani ne a ranar Alhamis a Abuja yayin taron Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa (NEC) karo na 160 wanda Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya jagoranta.<\/p>\n<p>Da yake yi wa manema labarai bayani bayan kammala taron Gwamnan Jihar Ondo Lucky Aiyedatiwa ya bayyana cewa <em>&#8220;wannan mataki ya yi daidai da kudirin gwamnatin Najeriya na ba da karin kulawa ga horar da jami&#8217;an Rundunar &#8216;Yan Sandan Najeriya.&#8221;<\/em><\/p>\n<p>Gwamna Aiyedatiwa ya jaddada cewa gwamnati ta sa ido sosai wajen inganta ayyukan rundunar &#8216;yan sandan kasar ta hanyar samar da ingantaccen horo ga ma&#8217;aikatanta.<\/p>\n<p>Ya ce <em>&#8220;Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa ta samu bayani daga kwamitinta na musamman da ke kula da gyaran cibiyoyin horar da &#8216;yan sanda inda aka sanar da ita cewa an riga an fara aiwatar da matakan da suka dace domin cimma burin inganta yanayin wadannan cibiyoyi.&#8221;<\/em><\/p>\n<p><em>&#8220;An kuma sanar da Majalisar cewa an riga an bayar da kwangilolin gyaran cibiyoyi 13 a sassa daban-daban na kasar kuma kashi 80 cikin 100 na &#8216;yan kwangilar sun riga sun karbi takardun amincewa da kwangilolin nasu.&#8221;<\/em><\/p>\n<p>KARANTA KUMA: Mataimakin Shugaban Kasa Shettima ya bukaci Majalisar Tattalin Arziki ta ci gaba da aiwatar da gyare-gyare.<\/p>\n<p>Mataimakin Gwamnan Jihar EnugU Ifeanyi Ossai wanda shi ma ya yi magana kan lamarin, ya bayyana cewa <em>&#8220;nan ba da jimawa ba za a saki \u0199arin ku\u0257a\u0257e ga &#8216;yan kwangilar.&#8221;<\/em><\/p>\n<p><em>&#8220;Ma&#8217;aikatar Ku\u0257i ta yi alkawarin cewa nan da mako mai zuwa za a saki sauran ku\u0257a\u0257en da ake bu\u0199ata don biyan &#8216;yan kwangilar DA kuma Majalisar na sa ran cewa &#8216;yan kwangilar da aka za\u0253a za su gudanar da ayyukan da aka damka musu cikin hanzari kamar yadda kwangilar ta tanada&#8221;<\/em> in ji shi.<\/p>\n<p>Har ila yau Mista Ossai ya ba &#8216;yan Najeriya tabbacin cewa za a ci gaba da gudanar da horo ga jami&#8217;an &#8216;yan sanda inda ya \u0199ara da cewa dukkan &#8216;yan \u0199asa suna da rawar da za su taka wajen tabbatar da tsaron \u0199asa ta hanyar ba da bayanai da ha\u0257in kai ga jami&#8217;an hukumomin tsaro.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>LADAN NASIDI.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamnatin Najeriya ta bayar da kwangilolin gyaran cibiyoyin horar da &#8216;yan sanda guda 13 a sassa daban-daban na kasar. An tsara shirin gyaran wanda zai dauki tsawon makonni uku domin shirya wadannan cibiyoyi don fara shirye-shiryen horarwa na rundunar &#8216;yan sandan Najeriya. An gabatar da wannan sabon bayani ne a ranar Alhamis a Abuja yayin &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3335,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[49,39],"tags":[],"class_list":["post-3332","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-fitattun-labarai","category-nigeria-news"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3332","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=3332"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3332\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3336,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3332\/revisions\/3336"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/3335"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=3332"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=3332"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=3332"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}