{"id":3216,"date":"2026-08-25T16:29:52","date_gmt":"2026-08-25T16:29:52","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=3216"},"modified":"2026-08-25T16:29:52","modified_gmt":"2026-08-25T16:29:52","slug":"shugaba-tinubu-ya-yi-allah-wadai-da-kksan-da-aka-yi-a-neja-ya-kuma-bayar-da-umarnin-ceto-wadanda-aka-sace","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/08\/25\/shugaba-tinubu-ya-yi-allah-wadai-da-kksan-da-aka-yi-a-neja-ya-kuma-bayar-da-umarnin-ceto-wadanda-aka-sace\/","title":{"rendered":"Shugaba Tinubu Ya Yi Allah-wadai Da kKsan Da Aka Yi A Neja Ya kuma Bayar Da Umarnin Ceto Wadanda Aka Sace"},"content":{"rendered":"<p><strong>Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah-wadai da sace tare da kashe fararen hula marasa laifi da wasu \u2018yan ta\u2019adda suka yi a Jihar Neja inda ya umurci Rundunar Soji da Rundunar \u2018Yan Sandan Najeriya da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da sauran hukumomin tsaro da leken asiri su hada karfi da karfe domin ceto wadanda aka sace din.<\/strong><\/p>\n<p>Wannan umarni yana cikin wata sanarwa ce da mai bai wa Shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru Mista Bayo Onanuga ya sanya wa hannu a ranar Talata.<\/p>\n<p>Yayin da yake jaddada cewa ba za a bar wadanda suka kai harin ba tare da an hukunta su ba Shugaban ya bayyana masu aikata laifin a matsayin makiyan zaman lafiya da \u2018yan adam tare da nanata cewa za a gurfanar da su gaban kuliya domin fuskantar shari\u2019a.<\/p>\n<p><em>&#8220;Wadanda suka kai wannan hari na rashin jaruntaka kan \u2018yan Najeriya marasa makami kuma makiyan zaman lafiya ne da makiyan \u2018yan adam kuma ba za su tsira ba&#8221;<\/em> in ji shi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>KARANTA KUMA: Sojoji Sun Dakile Kokarin \u2018Yan Ta\u2019adda na Sace Mutane a Zamfara<\/p>\n<p>Ya mika sakon ta\u2019aziyya ga iyalan wadanda aka kashe tare da ba wa \u2018yan uwan \u200b\u200bwadanda aka sace tabbacin cewa gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai an ceto \u2018yan uwansu cikin aminci.<\/p>\n<p><em>&#8220;Ba ku kadai ba ne. Daukacin al\u2019ummar kasar nan suna tare da ku cikin wannan hali na bakin ciki. Ba za mu huta ba har sai an dawo muku da \u2018ya\u2019yanku maza da mata da iyayenku mata da maza, cikin aminci&#8221;<\/em> in ji Shugaban.<\/p>\n<p>Ya kuma umurci shugabannin hukumomin tsaro da su rika ba da bayanai akai-akai game da aikin ceto har sai an gano dukkan wadanda aka sace.<\/p>\n<p>Yayin da yake sake jaddada kudirin gwamnati na kare rayuka da al&#8217;ummomi Shugaba Tinubu ya bayyana cewa ayyukan ta&#8217;addanci ba za su tsoratar da kasar ba.<\/p>\n<p><em>&#8220;Ta&#8217;addanci ba zai tsoratar da Najeriya ba. Za mu kare al&#8217;ummarmu mu kare yankunanmu tare da mutunta tsarkin rayuwar dan Adam&#8221;<\/em> in ji shi.<\/p>\n<p>Shugaban ya kuma bai wa gwamnatin Jihar Neja da al&#8217;ummomin da abin ya shafa tabbacin goyon bayan Gwamnatin Tarayya wajen ayyukan farfadowa da tallafi da kuma karfafa tsaro.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Ladan Nasidi.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah-wadai da sace tare da kashe fararen hula marasa laifi da wasu \u2018yan ta\u2019adda suka yi a Jihar Neja inda ya umurci Rundunar Soji da Rundunar \u2018Yan Sandan Najeriya da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da sauran hukumomin tsaro da leken asiri su hada karfi da karfe domin &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3219,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[49],"tags":[],"class_list":["post-3216","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-fitattun-labarai"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3216","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=3216"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3216\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3220,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3216\/revisions\/3220"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/3219"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=3216"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=3216"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=3216"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}