{"id":3197,"date":"2026-08-25T08:48:00","date_gmt":"2026-08-25T08:48:00","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=3197"},"modified":"2026-08-25T08:48:00","modified_gmt":"2026-08-25T08:48:00","slug":"yan-sanda-sun-ceto-mutane-75-da-aka-sace-a-kaduna","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/08\/25\/yan-sanda-sun-ceto-mutane-75-da-aka-sace-a-kaduna\/","title":{"rendered":"Yan Sanda Sun  Ceto Mutane 75 Da Aka Sace A Kaduna"},"content":{"rendered":"<p><strong>Rundunar &#8216;Yan Sandan Jihar Kaduna ta ceto mutane 75 da wasu &#8216;yan bindiga suka yi garkuwa da su kusa da Birnin Gwari a jihar.<\/strong><\/p>\n<p>Mutanen wadanda suka hada da maza mata da yara &#8216;yan kabilar Fulani suna tafiya ne a cikin motocin haya lokacin da &#8216;yan bindiga dauke da bindigogin AK-47 da sauran makamai masu karfi suka tare su a kauyen Folwaya kusa da Birnin Gwari a ranar 19 ga watan Agusta, 2026.<\/p>\n<p>A cewar rundunar &#8216;yan sandan an sanar da su game da lamarin da misalin karfe 5:30 na yamma ta hannun kungiyar direbobi da ma&#8217;aikatan sufuri ta kasa (NURTW) reshen Birnin Gwari.<\/p>\n<p>Bayan samun rahoton an tura wata kwararriyar tawagar &#8216;yan sanda daga sashen Birnin Gwari zuwa wurin nan take.<\/p>\n<p>An bayyana cewa masu garkuwar sun kai wadanda suka sace din cikin daji tare da boye su a wani kogo da ke cikin tsaunuka.<\/p>\n<p>Sai dai &#8216;yan bindigar sun tsere bayan sun hango jami&#8217;an &#8216;yan sandan da ke dauke da makamai masu karfi inda suka bar wadanda suka yi garkuwa da su a wurin.<\/p>\n<p>Daga bisani aka ceto mutanen 75 din ba tare da sun samu wani rauni ba.<\/p>\n<p>KARANTA KUMA: Sanatocin Arewa Sun Yi Kira da a Hanzarta Kafa &#8216;Yan Sandan Jiha<\/p>\n<p>Kwamishinan &#8216;Yan Sandan Jihar Kaduna CP Rabiu Muhammad ya yaba wa kungiyar NURTW reshen Birnin Gwari bisa samar da muhimman bayanai a kan lokaci wadanda suka taimaka wajen nasarar aikin ceto mutanen.<\/p>\n<p>Ya kuma yaba wa Kwamandan &#8216;Yan Sanda na yankin Birnin Gwari da jami&#8217;ansa bisa daukar mataki cikin gaggawa da kwarewa.<\/p>\n<p>Kwamishinan ya yi kira ga mazauna yankin da su ci gaba da kasancewa cikin shiri da kuma sanar da &#8216;yan sanda duk wani motsi ko aiki na shakku ba tare da bata lokaci ba.<\/p>\n<p>Ya kuma gargadi jama&#8217;a game da daukar doka a hannunsu inda ya yi nuni da cewa irin wadannan ayyuka na iya haifar da asarar rayukan marasa laifi.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Safina Umar Farouk.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Rundunar &#8216;Yan Sandan Jihar Kaduna ta ceto mutane 75 da wasu &#8216;yan bindiga suka yi garkuwa da su kusa da Birnin Gwari a jihar. Mutanen wadanda suka hada da maza mata da yara &#8216;yan kabilar Fulani suna tafiya ne a cikin motocin haya lokacin da &#8216;yan bindiga dauke da bindigogin AK-47 da sauran makamai masu &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3200,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[39],"tags":[],"class_list":["post-3197","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-nigeria-news"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3197","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=3197"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3197\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3201,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3197\/revisions\/3201"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/3200"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=3197"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=3197"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=3197"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}