{"id":3171,"date":"2026-08-24T14:37:34","date_gmt":"2026-08-24T14:37:34","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=3171"},"modified":"2026-08-24T14:37:34","modified_gmt":"2026-08-24T14:37:34","slug":"apc-za-ta-tabbatar-da-sake-zaben-tinubu-yari","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/08\/24\/apc-za-ta-tabbatar-da-sake-zaben-tinubu-yari\/","title":{"rendered":"APC Za Ta Tabbatar Da Sake Zaben Tinubu \u2013 Yari"},"content":{"rendered":"<p><strong>Darakta-Janar na Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na jam&#8217;iyyar All Progressives Congress (APC) Sanata Abdul\u2019aziz Yari ya bayyana cewa jam&#8217;iyyar za ta cika alkawuran da ta yi a yakin neman zabe tare da yin aiki tukuru domin ganin an sake zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2027.<\/strong><\/p>\n<p>Yari ya yi wannan jawabi ne a Abuja bayan da magoya bayansa suka yi masa tarba ta musamman sakamakon dawowarsa daga wata tafiya ta kasashen waje.<\/p>\n<p>Da aka tambaye shi yadda yake ji game da nadin da aka yi masa da kuma tarbar da magoya bayansa suka yi masa a fadin kasar Yari ya bayyana cewa yana jin alfahari da amincewar da Shugaba Tinubu ya nuna a gare shi.<\/p>\n<p><em>&#8220;Ina jin alfahari. Ina jin alfahari da wannan amincewa da Shugaban Kasa ya yi mini. Kuma In sha Allahu zan yi iya bakin kokarina wajen ganin mun cimma nasara&#8221;<\/em> in ji shi.<\/p>\n<p>Ya ce bukukuwan da ake yi a yanzu farko ne kawai, inda ya jaddada cewa hakikanin murnar za ta zo ne bayan zaben 2027. <em>&#8220;A yau komai na murna ne. Amma hakikanin murnar za ta zo ne a watan Janairu idan mun cimma nasarar da ake bukata.&#8221;<\/em><\/p>\n<p>Yari ya yi kira ga magoya bayan APC da su hada kai wajen goyon bayan Tinubu tare da yin addu&#8217;ar samun nasarar kwamitin yakin neman zaben.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>KARANTA KUMA: Shugaban Jam&#8217;iyyar APC na Kasa ya nemi afuwar &#8216;ya&#8217;yan jam&#8217;iyyar na jihar Oyo da ke da korafi<\/p>\n<p><em>&#8220;Wannan lokaci ne da ya kamata mu ha\u0257u domin tabbatar da cewa muna yin abu \u0257aya. Wannan abu \u0257aya shine Bola Tinubu.&#8221;<\/em> Yari ya jaddada.<\/p>\n<p>Dangane da abin da &#8216;yan Najeriya ya kamata su zata daga APC Yari ya yi al\u0199awarin cewa jam&#8217;iyyar za ta ci gaba da bin manufofinta da alkawuran yakin neman za\u0253e.<\/p>\n<p><em>&#8220;Duk abin da muka fa\u0257a a lokacin kamfen mu cika manufofinmu mu cika al\u0199awarinmu domin za\u0253en ba na yau ba ne.&#8221;<\/em><\/p>\n<p>Tsohon gwamnan jihar Zamfara ya ce APC ta yi imanin cewa Tinubu zai sake samun wa&#8217;adi a kan mulki a 2027.<\/p>\n<p>Yari ya kuma bayyana kwarin gwiwar cewa APC za ta ci gaba da kasancewa jam&#8217;iyyar da ke mulki a Najeriya bayan wa&#8217;adin Tinubu na biyu.<\/p>\n<p><em>&#8220;Muna addu&#8217;ar jam&#8217;iyyar ta ci gaba da mulki bayan Tinubu a matsayin jam&#8217;iyyar da za ta jagoranci \u0199asar.&#8221;<\/em><\/p>\n<p>Ya ce jajircewar jam&#8217;iyyar na cika alkawarinta zai zama babban abin da zai sa ta yi kamfen \u0257inta yayin da yake addu&#8217;ar Allah ya ba wa Shugaba Tinubu hikimar jagoranci \u0199asar da kuma cika alkawuran da aka yi wa &#8216;yan Najeriya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>LADAN NASIDI.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Darakta-Janar na Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na jam&#8217;iyyar All Progressives Congress (APC) Sanata Abdul\u2019aziz Yari ya bayyana cewa jam&#8217;iyyar za ta cika alkawuran da ta yi a yakin neman zabe tare da yin aiki tukuru domin ganin an sake zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2027. Yari ya yi wannan jawabi ne &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":3174,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[47],"tags":[],"class_list":["post-3171","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-politics"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3171","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=3171"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3171\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":3175,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/3171\/revisions\/3175"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/3174"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=3171"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=3171"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=3171"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}