{"id":2972,"date":"2026-08-18T11:35:09","date_gmt":"2026-08-18T11:35:09","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=2972"},"modified":"2026-08-18T11:35:09","modified_gmt":"2026-08-18T11:35:09","slug":"shugaban-kasar-zambia-ya-sake-lashe-zabe-domin-waadi-na-biyu","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/08\/18\/shugaban-kasar-zambia-ya-sake-lashe-zabe-domin-waadi-na-biyu\/","title":{"rendered":"Shugaban kasar Zambia Ya Sake Lashe Zabe Domin Wa&#8217;adi Na Biyu"},"content":{"rendered":"<p><strong>Hukumar zaben Zambia ta sanar da cewa an sake zaben Shugaba Hakainde Hichilema domin wa&#8217;adi na biyu na shekaru biyar bayan ya samu kashi 60 cikin dari na jimillar kuri&#8217;un da aka kada.<\/strong><\/p>\n<p>An yi tsammanin nasarar Hichilema inda babban abokin hamayyarsa Brian Mundubile ya samu kashi 38 cikin dari na kuri&#8217;un da aka kada sauran &#8216;yan takara 12 kuwa sun yi nisa sosai a baya.<\/p>\n<p>Sakamakon ya zo ne bayan wani tsari mai cike da takaddama inda Mundubile mai shekaru 55 ya fara ikirarin samun nasara tare da zargin cewa an samu matsaloli ko magudi a yayin zaben duk da cewa bai gabatar da hujjoji ba.<\/p>\n<p><img decoding=\"async\" src=\"https:\/\/von.gov.ng\/wp-content\/uploads\/2026\/08\/c364cf20-9ac3-11f1-8ebb-7f566bc6488f.jpg-300x169.webp\" \/><\/p>\n<p>Haka kuma lamarin ya biyo bayan kama wasu manyan &#8216;yan adawa a wani samame da aka kai ranar Juma&#8217;a inda hukumomi suka zarge su da shirin tayar da tarzoma. Mundubile ya bayyana zargin a matsayin karya.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>KARANTA KUMA:<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>A cikin wata sanarwa bayan an bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara Hichilema mai shekaru 64 ya ce <em>&#8220;Mun ji matukar godiya da tawali&#8217;u bisa amincewar da kuka nuna mana.&#8221;<\/em><\/p>\n<p>Ya ce zaben ya nuna cewa Zambia kasa ce mai zaman lafiya, bin doka da oda, tare da kasancewa <em>&#8220;kasa mai tsarin dimokradiyya da ke warware sabanin ra&#8217;ayi ta hanyar kada kuri&#8217;a, ba ta wata hanya ta daban ba.&#8221;<\/em><\/p>\n<p><em>&#8220;Ga &#8216;yan kasa da suka fi goyon bayan ra&#8217;ayoyin da abokan hamayyarmu suka gabatar mun ji ku, kuma za mu ci gaba da yi muku aiki&#8221;<\/em> in ji shi.<\/p>\n<p>Daruruwan magoya bayan Hichilema, wadanda suka sanya tufafi masu launin ja na jam&#8217;iyyarshi ta United Party for National Development (UPND) sun cika titunan babban birnin kasar Lusaka domin yin murna bayan sanar da sakamakon zaben.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>BBC\/LADAN NASIDI<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Hukumar zaben Zambia ta sanar da cewa an sake zaben Shugaba Hakainde Hichilema domin wa&#8217;adi na biyu na shekaru biyar bayan ya samu kashi 60 cikin dari na jimillar kuri&#8217;un da aka kada. An yi tsammanin nasarar Hichilema inda babban abokin hamayyarsa Brian Mundubile ya samu kashi 38 cikin dari na kuri&#8217;un da aka kada &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":2975,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[42],"tags":[],"class_list":["post-2972","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-afica-news"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2972","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=2972"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2972\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2976,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2972\/revisions\/2976"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/2975"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=2972"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=2972"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=2972"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}