{"id":2904,"date":"2026-08-17T11:17:30","date_gmt":"2026-08-17T11:17:30","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=2904"},"modified":"2026-08-17T11:17:30","modified_gmt":"2026-08-17T11:17:30","slug":"shugaba-tinubu-ya-taya-gwamna-adeleke-murnar-nasarar-zabe","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/08\/17\/shugaba-tinubu-ya-taya-gwamna-adeleke-murnar-nasarar-zabe\/","title":{"rendered":"Shugaba Tinubu Ya Taya Gwamna Adeleke Murnar Nasarar Zabe"},"content":{"rendered":"<p><strong>Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yaba da nasarar da Gwamna Ademola Adeleke ya samu a zaben gwamnan jihar Osun da aka kammala kwanan nan inda ya bayyana hakan a matsayin tabbacin cewa dimokuradiyya za ta ci gaba da bunkasa a kasar karkashin gwamnatin jam&#8217;iyyar All Progressives Congress (APC).<\/strong><\/p>\n<p>Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Mista Bayo Onanuga, ya sanya wa hannu tare da fitarwa a ranar Lahadi.<\/p>\n<p>Har ila yau ya yaba wa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da hukumomin tsaro bisa gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali da gaskiya wanda ya haifar da fitowar wanda ya yi nasara a fili.<\/p>\n<p>Ya ce: <em>&#8220;Na kira Gwamna Ademola Adeleke a yau domin taya shi murnar nasarar da ya samu a zaben jihar Osun. Nasarar da ya samu ta sake tabbatar da kwarin gwiwar da al&#8217;ummar jihar Osun ke da shi a gare shi.&#8221;<\/em><\/p>\n<p>Shugaban ya kuma bukaci Gwamna Adeleke da ya hada kan al&#8217;ummar jihar Osun tare da tattara su domin samun ci gaba, kwanciyar hankali da bunkasar zamantakewa da tattalin arziki ba tare da la&#8217;akari da zabin siyasar da suka yi a lokacin zaben ba.<\/p>\n<p><img decoding=\"async\" src=\"https:\/\/von.gov.ng\/wp-content\/uploads\/2026\/08\/54ced14ac9ec1eafc02607cedd35c51f2d31ea35c8ec1bf51e48909cacf9089a-300x230.webp\" \/><\/p>\n<p><em>\u201cIna yi masa fatan samun nasara mai girma yayin da yake shirin jagorantar jihar na tsawon shekaru hudu masu zuwa. Yanzu da ya yi nasara dole ne Gwamna Adeleke ya hada kan al\u2019ummar jihar Osun tare da tattara su domin samun ci gaba kwanciyar hankali da kuma ci gaban zamantakewa da tattalin arziki ba tare da la\u2019akari da zabin siyasar da suka yi a lokacin zaben ba.<\/em><\/p>\n<p><em>\u201cIna yaba wa jaruntaka da kuma nuna halin girma da sauran \u2018yan takarar zaben suka yi. Shigarsu takarar ta zurfafa tare da inganta al\u2019adun dimokuradiyya a kasarmu. Sakamakon zaben yana nuna ra\u2019ayin jama\u2019a kuma shaida ce mai kyau da ke tabbatar da cewa dimokuradiyya za ta ci gaba da bunkasa a kasarmu\u201d<\/em> in ji Shugaba Tinubu.<\/p>\n<p>An ayyana Gwamna Ademola Adeleke dan takarar jam\u2019iyyar Accord Party a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Osun na ranar 15 ga watan Agusta bayan ya samu kuri\u2019u 511,067 tare da lashe kananan hukumomi 19 cikin 30 na jihar inda ya doke babban abokin hamayyarsa, Bola Oyebamiji na jam\u2019iyyar All Progressives Congress wanda ya lashe kananan hukumomi 11.<\/p>\n<p>KARANTA KARIN BAYANI: Jami\u2019in hukumar INEC mai kula da sanar da sakamakon zaben Farfesa Joshua Olalekan Ogunwole<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>LADAN NASIDI.<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yaba da nasarar da Gwamna Ademola Adeleke ya samu a zaben gwamnan jihar Osun da aka kammala kwanan nan inda ya bayyana hakan a matsayin tabbacin cewa dimokuradiyya za ta ci gaba da bunkasa a kasar karkashin gwamnatin jam&#8217;iyyar All Progressives Congress (APC). Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":2,"featured_media":2907,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[49,47],"tags":[],"class_list":["post-2904","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-fitattun-labarai","category-politics"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2904","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/2"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=2904"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2904\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2908,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2904\/revisions\/2908"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/2907"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=2904"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=2904"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=2904"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}