{"id":2762,"date":"2026-08-10T08:27:54","date_gmt":"2026-08-10T08:27:54","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=2762"},"modified":"2026-08-10T08:27:54","modified_gmt":"2026-08-10T08:27:54","slug":"ododo-ya-yaba-da-salon-shugabancin-na-shugaban-apc-da-hada-kan-jamaa-ya-yin-cika-shekaru-58","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/08\/10\/ododo-ya-yaba-da-salon-shugabancin-na-shugaban-apc-da-hada-kan-jamaa-ya-yin-cika-shekaru-58\/","title":{"rendered":"Ododo Ya Yaba Da Salon Shugabancin Na Shugaban APC Da Hada Kan Jama&#8217;a Ya Yin Cika Shekaru 58."},"content":{"rendered":"<p><strong>Gwamna Ahmed Ododo na jihar Kogi ya taya Shugaban jam&#8217;iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, murnar cika shekaru 58 da haihuwa, inda ya bayyana shi a matsayin shugaba mai sadaukarwa wanda ke haifar da kwanciyar hankali da ci gaba a cikin jam&#8217;iyyar mai mulki.<\/strong><\/p>\n<p>A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai da Sadarwa, Mista Femi Fanwo, ya fitar a ranar Asabar da ta gabata, a Lokoja, Ododo ya ce jagorancin Yilwatda ya ci gaba da bayar da gagarumar gudunmawa ga hadin kai, dunkulewar jam&#8217;iyya, da ci gaban APC.<\/p>\n<p>Gwamnan ya bayyana cewa sake zaben Yilwatda a babban taron jam&#8217;iyyar na kasa ya nuna karara irin amincewar da mambobi da masu ruwa da tsaki na jam&#8217;iyyar a fadin kasar suka nuna masa.<\/p>\n<p>KARANTA KUMA: Gwamna Ododo ya yaba da tsarin tsaro na Shugaba Tinubu<\/p>\n<p>A cewar Ododo, Yilwatda ya yi amfani da gogewarsa, zurfin iliminsa, da fahimtar siyasar zamani wajen tafiyar da harkokin jam&#8217;iyyar mai mulki a wani muhimmin lokaci na ci gaban siyasar kasar.<\/p>\n<p><em><strong>&#8220;A madadin iyalina, gwamnati, da kuma al&#8217;ummar jihar Kogi, ina taya shugabanmu na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, murnar zagayowar ranar haihuwarsa ta cika shekaru 58,&#8221;<\/strong><\/em> in ji gwamnan.<\/p>\n<p>Ododo ya kara yaba masa bisa nuna jagoranci mai cike da jaruntaka da balaga a wani muhimmin lokaci na tafiyar dimokradiyyar kasar.<\/p>\n<p>Ya kara da cewa, sadaukarwar da Yilwatda ke yi wajen tabbatar da hadin kan jam&#8217;iyya ta yi daidai da manufar <em><strong>&#8216;Renewed Hope Agenda&#8217;<\/strong><\/em> (Sabon Fatan Ci Gaba) ta Shugaba Bola Tinubu.<\/p>\n<p><em><strong>&#8220;Musamman ma ina yaba kokarinka wajen karfafa tsarin jam&#8217;iyyarmu da kuma samar da jagorancin da ake bukata domin ci gaba da hada kan APC da kuma mayar da hankali kan aiwatar da manufar &#8216;Renewed Hope Agenda&#8217; ta babban shugabanmu, Shugaba Tinubu, GCFR,&#8221;<\/strong><\/em> in ji Ododo.<\/p>\n<p>Gwamnan ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa jagorancin Yilwatda zai ci gaba da zama ginshiki yayin da APC ke karfafa nasarorin da ta samu tare da shiryawa domin kalubale da damammakin nan gaba.<\/p>\n<p>Ya yi addu&#8217;ar Allah Madaukakin Sarki Ya ba shugaban jam&#8217;iyyar na kasa karin shekaru masu yawa cikin koshin lafiya, hikima, da gamsuwa, tare da samun karin nasarori a ayyukansa na bauta wa jam&#8217;iyya da kasa baki daya. <em><strong>\u201cAllah Madaukakin Sarki Ya ci gaba da ba ku karfi, Ya albarkace ku da lafiya mai kyau, tare da ba ku karin shekaru masu yawa na ci gaba da gudanar da ayyuka masu amfani ga babbar jam\u2019iyyarmu, kasarmu da kuma bil\u2019adama baki daya.<\/strong><\/em><\/p>\n<p><em><strong>Murnar cika shekaru 58 da haihuwa, Mai Girma. Barka da wannan rana, kuma Allah Ya sa a ci gaba da samun irinta cikin farin ciki,\u201d<\/strong><\/em> in ji gwamnan.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>NAN\/Aisha.Yahaya Lagos<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Gwamna Ahmed Ododo na jihar Kogi ya taya Shugaban jam&#8217;iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, murnar cika shekaru 58 da haihuwa, inda ya bayyana shi a matsayin shugaba mai sadaukarwa wanda ke haifar da kwanciyar hankali da ci gaba a cikin jam&#8217;iyyar mai mulki. A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai da Sadarwa, &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":3,"featured_media":2765,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[47],"tags":[],"class_list":["post-2762","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-politics"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2762","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/3"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=2762"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2762\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2767,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2762\/revisions\/2767"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/2765"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=2762"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=2762"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=2762"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}