{"id":2755,"date":"2026-08-10T08:04:15","date_gmt":"2026-08-10T08:04:15","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=2755"},"modified":"2026-08-10T08:04:15","modified_gmt":"2026-08-10T08:04:15","slug":"yan-sanda-ndlea-da-sauransu-sun-yi-kira-da-a-gudanar-da-zaben-osun-ba-tare-da-tashin-hankali-ba","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/08\/10\/yan-sanda-ndlea-da-sauransu-sun-yi-kira-da-a-gudanar-da-zaben-osun-ba-tare-da-tashin-hankali-ba\/","title":{"rendered":"Yan Sanda, NDLEA Da Sauransu Sun Yi Kira da a Gudanar Da Zaben Osun Ba Tare Da Tashin Hankali Ba"},"content":{"rendered":"<p><strong>Rundunar &#8216;Yan Sandan Najeriya (NPF), tare da hadin gwiwar Kungiyar Daliban Najeriya ta Kasa (NANS), Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), Shirin Yi wa Kasa Hidima na Matasa (NYSC) da sauran masu ruwa da tsaki, sun yi kira da a gudanar da zaben gwamna cikin lumana da rashin tashin hankali a Jihar Osun.<\/strong><\/p>\n<p>An yi wannan kiran ne a ranar Asabar da ta gabata ,yayin wani tattakin wayar da kan jama&#8217;a a birnin Osogbo mai taken <strong>&#8220;<em>Tattakin Wayar da Kai:<\/em> <\/strong>A Ce A&#8217;a ga <em><strong>Tashin Hankali a Zabe,&#8221;<\/strong> <\/em>wanda shirin &#8216;Yan Sanda na Yaki da Kungiyoyin Asiri da Sauran Munanan Ayyuka (POCACOV) ya shirya.<\/p>\n<p>Da yake jawabi a wajen taron, Mataimakin Sufeton &#8216;Yan Sanda na Kasa (AIG), Akinyele Fasuba, ya tabbatar wa al&#8217;ummar jihar cewa &#8216;yan sanda sun shirya tsaf don tabbatar da gudanar da zaben gwamna cikin lumana, wanda aka tsara gudanarwa a ranar 15 ga watan Agusta, 2026.<\/p>\n<p><img loading=\"lazy\" decoding=\"async\" class=\"alignnone size-medium wp-image-2759\" src=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/08\/IMG-20260809-WA0019-768x576-1-300x225.jpg\" alt=\"\" width=\"300\" height=\"225\" srcset=\"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/08\/IMG-20260809-WA0019-768x576-1-300x225.jpg 300w, https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-content\/uploads\/2026\/08\/IMG-20260809-WA0019-768x576-1.jpg 768w\" sizes=\"auto, (max-width: 300px) 100vw, 300px\" \/><\/p>\n<p>KARANTA KUMA: &#8216;Yan Sandan Najeriya da Kungiyoyin Farar Hula Sun Yi Alkawarin Zabe Mai Zaman Lafiya a Osun<\/p>\n<p>Fasuba ya bayyana cewa Rundunar &#8216;Yan Sandan Najeriya, a matsayinta na babban hukumar da ke da alhakin tsaron cikin gida, ta dauki matakan da suka dace don tabbatar da gudanar da zabe cikin lumana.<\/p>\n<p>Ya yaba wa shirin POCACOV bisa shirya tattakin wayar da kan jama&#8217;a kafin zaben, inda ya ce an yi hakan ne domin fadakar da jama&#8217;a, musamman matasa, game da hadarin kungiyoyin asiri, ayyukan &#8216;yan daba, shan miyagun kwayoyi da sauran ayyukan laifi da ka iya kawo cikas ga tsarin zaben.<\/p>\n<p>Ya kara da cewa &#8216;yan sanda ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen daukar tsauraran matakai kan duk wani mutum ko kungiya da ayyukansu za su iya barazana ga zaman lafiyar zaben.<\/p>\n<p>Haka kuma, Kwamishinan &#8216;Yan Sandan Jihar Osun, Ibrahim Gotan, ya tabbatar wa mazauna jihar cewa &#8216;yan sandan Najeriya da sauran hukumomin tsaro sun shirya tsaf don samar da isasshen tsaro yayin zaben.<\/p>\n<p>Sai dai, Kwamishinan ya yi kira ga mazauna jihar, &#8216;yan siyasa, da sauran masu ruwa da tsaki da su mai da hadin kai da goyon baya domin karfafa kokarin hukumomin tsaro. <em><strong>&#8220;Muna bukatar goyon baya da hadin kan kowa da kowa.<\/strong><\/em><\/p>\n<p>Za a samar da isasshen tsaro a dukkan rumfunan zabe na jihar. Kowace rumfar zabe za ta samu kulawar akalla jami&#8217;an &#8216;yan sanda hudu, tare da jami&#8217;an sauran hukumomin tsaro.<\/p>\n<p><em><strong>&#8220;Mun zo nan ne domin tabbatar wa al&#8217;ummar Jihar Osun cewa su fito su gudanar da hakkinsu na zabe ba tare da tsoro ko barazana daga kowa ba.&#8221;<\/strong><\/em><\/p>\n<p>Gotan ya ba da tabbacin cewa &#8216;yan sanda za su nuna rashin bangaranci ko kadan, kuma zaben zai kasance mai inganci, &#8216;yanci, da adalci.<\/p>\n<p>A wani bangaren kuma, Babban Mai Gudanarwa na Shirin &#8216;Yan Sanda na Yaki da Kungiyoyin Asiri da Sauran Munanan Ayyuka (POCACOV), SP Orvenonne Ikwen, ta bayyana irin hadin gwiwar da kungiyoyi irin su NANS, NDLEA, NYSC da sauran masu ruwa da tsaki suka bayar wajen ganin an gudanar da zabe cikin lumana.<\/p>\n<p>Ikwen ta ce Babban Sufeton &#8216;Yan Sanda (IGP), Olatunji Ridwan Disu, ya umurci kungiyar da ta shirya tattakin wayar da kan jama&#8217;a a matsayin wani bangare na kokarin tabbatar wa mazauna jihar cewa &#8216;yan sanda sun kuduri aniyar ganin an gudanar da zabe cikin lumana da inganci.<\/p>\n<p>Ta bayyana cewa an kuma tsara wannan yakin neman wayar da kan ne domin karfafa gwiwar masu zabe su gudanar da hakkinsu na kada kuri&#8217;a cikin lumana.<\/p>\n<p>&#8220;<em><strong>Babban Sufeton &#8216;Yan Sanda, IGP Olatunji Ridwan Disu, ya umurce mu da mu shirya tattakin wayar da kan jama&#8217;a kafin zaben gwamna a Jihar Osun domin tabbatar wa al&#8217;ummar jihar cewa zaben zai kasance mai &#8216;yanci da inganci, ba tare da wata barazana ko tsoratarwa ba.&#8221;<\/strong><\/em> Saboda haka, ta yi kira ga jama&#8217;a da su kada kuri&#8217;a maimakon yin fada, inda ta jaddada cewa yakin neman zaben ya yi tir da duk wani nau&#8217;i na tashin hankali.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Aisha.Yahaya, Lagos<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Rundunar &#8216;Yan Sandan Najeriya (NPF), tare da hadin gwiwar Kungiyar Daliban Najeriya ta Kasa (NANS), Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), Shirin Yi wa Kasa Hidima na Matasa (NYSC) da sauran masu ruwa da tsaki, sun yi kira da a gudanar da zaben gwamna cikin lumana da rashin tashin hankali &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":3,"featured_media":2758,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[47],"tags":[],"class_list":["post-2755","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-politics"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2755","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/3"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=2755"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2755\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2761,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2755\/revisions\/2761"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/2758"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=2755"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=2755"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=2755"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}