{"id":2736,"date":"2026-08-09T14:16:27","date_gmt":"2026-08-09T14:16:27","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=2736"},"modified":"2026-08-09T14:16:27","modified_gmt":"2026-08-09T14:16:27","slug":"ivory-coast-ta-karbi-gangar-isar-da-sako-a-mulkin-mallaka","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/08\/09\/ivory-coast-ta-karbi-gangar-isar-da-sako-a-mulkin-mallaka\/","title":{"rendered":"Ivory Coast Ta Karbi Gangar Isar Da Sako A Mulkin Mallaka"},"content":{"rendered":"<p><strong>Kasar Ivory Coast ta karbi gangar gargajiya mai suna Djidji Ayokwe\u2014wacce ake kira gangar da ke <em>&#8220;magana&#8221;\u2014<\/em>fiye da shekaru dari bayan da sojojin mulkin mallaka na Faransa suka kwace ta; wannan lamari na wakiltar wani muhimmin ci gaba a kokarin da ake yi na dawo da kayan tarihi da al&#8217;adun Afirka.<\/strong><\/p>\n<p>Al&#8217;ummar yankin da gangar ta fito sun tarbe ta a ranar Juma&#8217;a Da ta gabata, yayin bukukuwan da suka gudana tare da bikin cika shekaru da samun &#8216;yancin kai na Ivory Coast. Gangar, wacce aka yi ta da katako, tana da tsawon mita uku da nauyin kusan kilogram 430.<\/p>\n<p>Asali, gangar Djidji Ayokwe ta al&#8217;ummar Ebrie ce, kuma ana amfani da ita wajen isar da sakonni, gargadin mazauna yankin game da hadari, kiran mutane zuwa yaki, da kuma tara kauyawa domin gudanar da muhimman bukukuwa.<\/p>\n<p>An mika wannan kayan tarihi ga Ivory Coast a hukumance a watan Fabrairu, sannan aka dawo da shi kasar a watan Maris ta hanyar amfani da jirgin sama na musamman da aka yi hayarta. An ajiye gangar a cikin wani babban akwatin katako har zuwa ranar Juma&#8217;a da ta gabata, lokacin da aka nuna ta ga jama&#8217;a a karon farko.<\/p>\n<p>An yi jigilar gangar ne a cikin akwati mai gilashi a gaba, wanda aka dora a kan wani dandali mai kayatarwa yayin jerin gwanon sojoji a unguwar Yopougon da ke Abidjan, kafin daga bisani a kai ta Adjame, yankin da aka fara kera ta.<\/p>\n<p>Ministar Al&#8217;adu ta Ivory Coast, Francoise Remarck, tare da shugabannin gargajiya da daruruwan mazauna yankin, sun taru domin karbar wannan kayan tarihi. Haka kuma, an gudanar da wani biki na gargajiya na zubar da ruwa ko abin sha a kasa domin girmama kakanni.<\/p>\n<p>Magajin garin Adjame, Farikou Soumahoro, ya bayyana dawowar gangar a matsayin lokaci na <em><strong>&#8220;babban alfahari,&#8221;<\/strong><\/em> inda ya jaddada cewa kare kayan tarihi da al&#8217;adu yana da matukar muhimmanci ga ci gaban kasa.<\/p>\n<p>Sojojin mulkin mallaka na Faransa sun kwace gangar Djidji Ayokwe a shekarar 1916, sannan suka kai ta Turai a shekarar 1929, inda aka ci gaba da nuna ta a birnin Paris na tsawon shekaru da dama.<\/p>\n<p>Ivory Coast ta nemi a dawo da ita a hukumance a shekarar 2018, a matsayin wani bangare na babban yakin neman dawo da kayan tarihi guda 148 da aka kwashe a lokacin mulkin mallaka.<\/p>\n<p>Ana sa ran za a nuna gangar a Gidan Tarihi na Wayewa (Museum of Civilisations) da ke Abidjan, wanda aka gyara na musamman domin ajiye wannan muhimmin kayan tarihi.<\/p>\n<p>Dawowar gangar wani bangare ne na yunkuri mai karfi a fadin Afirka na dawo da kayan tarihi da al&#8217;adu masu daraja da aka kwashe a zamanin mulkin mallaka. Kasashe irin su Senegal da Benin suma sun nemi a dawo musu da muhimman kayan tarihi da ake ajiye su a gidajen tarihi da tarin kayan tarihi na kasashen waje.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Aisha.Yahaya,\u00a0 Lagos<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Kasar Ivory Coast ta karbi gangar gargajiya mai suna Djidji Ayokwe\u2014wacce ake kira gangar da ke &#8220;magana&#8221;\u2014fiye da shekaru dari bayan da sojojin mulkin mallaka na Faransa suka kwace ta; wannan lamari na wakiltar wani muhimmin ci gaba a kokarin da ake yi na dawo da kayan tarihi da al&#8217;adun Afirka. Al&#8217;ummar yankin da gangar &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":3,"featured_media":2739,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[42],"tags":[],"class_list":["post-2736","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-afica-news"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2736","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/3"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=2736"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2736\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2741,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2736\/revisions\/2741"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/2739"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=2736"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=2736"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=2736"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}