{"id":2709,"date":"2026-08-09T11:59:34","date_gmt":"2026-08-09T11:59:34","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=2709"},"modified":"2026-08-09T11:59:34","modified_gmt":"2026-08-09T11:59:34","slug":"shugabannin-serbia-da-ukraine-na-neman-karfafa-dangantaka-tattalin-arziki-tsakani-kasashen-biyu","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/08\/09\/shugabannin-serbia-da-ukraine-na-neman-karfafa-dangantaka-tattalin-arziki-tsakani-kasashen-biyu\/","title":{"rendered":"Shugabannin Serbia Da Ukraine Na Neman Karfafa Dangantaka Tattalin Arziki Tsakani Kasashen Biyu"},"content":{"rendered":"<p><strong>Shugaban kasar Serbia, Aleksandar Vu\u010di\u0107, ya bayyana a ranar Asabar cewa kasarsa ta sake jaddada goyon bayanta ga &#8216;yancin kai da kuma mutuncin yankunan kasar Ukraine, yayin da take kokarin karfafa hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.<\/strong><\/p>\n<p>Vu\u010di\u0107 ya bayyana hakan ne yayin ziyarar kwana biyu da shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelenskiy, ya kai birnin Belgrade\u2014ziyarar farko da ya yi wa Serbia tun bayan karbar mulki a shekarar 2019.<\/p>\n<p>Serbia ta yi Allah-wadai da mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, amma ta ki sanya takunkumi kan Moscow, inda ta ci gaba da kiyaye dadaddun alakar siyasa da tattalin arziki da kawarta na dada.<\/p>\n<p>Har ila yau, Belgrade ta dogara matuka kan Rasha wajen samun iskar gas, yayin da Vu\u010di\u0107 ke ci gaba da daidaita burin Serbia na shiga kungiyar Tarayyar Turai (EU) da kuma kusancin dangantakarta da Moscow.<\/p>\n<p>Vu\u010di\u0107 ya ce Serbia za ta ci gaba da goyon bayan mutuncin yankunan Ukraine, ciki har da yankunan da Rasha ta kwace tun shekarar 2014.<\/p>\n<p><em><strong>&#8220;Ba ku taba jin wata mummunar magana game da kasarmu ba, ko daga Volodymyr Zelenskiy ko daga wani mutum daban (a Ukraine), kuma ina matukar godiya ga abokanmu na Ukraine saboda hakan,&#8221;<\/strong><\/em> in ji Vu\u010di\u0107.<\/p>\n<p>Ya bayyana cewa Serbia za ta goyi bayan yunkurin Ukraine na shiga kungiyar Tarayyar Turai, duk da cewa ya nuna shakku kan ko kasashen biyu za su samu damar shiga kungiyar cikin sauri.<\/p>\n<p>Shugabannin biyu sun kuma amince su karfafa alakar tattalin arziki tare da yin aiki don kammala yarjejeniyar ciniki cikin &#8216;yanci kafin karshen shekara.<\/p>\n<p>KARANTA KUMA: Burnham ya sake jaddada goyon bayan Birtaniya mai karfi ga Ukraine<\/p>\n<p>Wannan yarjejeniya tana da muhimmanci ga kokarin Serbia na shiga kungiyar Ciniki ta Duniya (WTO), kuma ana daukarta a matsayin sharadi na shiga kungiyar Tarayyar Turai a nan gaba. Ukraine ta dakatar da yarjejeniyar tun shekarar 2005 saboda damuwa game da iyakar yawan kayan noma da za a iya fitarwa da kuma harajin kwastam.<\/p>\n<p>Zelenskiy ya ce tattaunawar da ya yi da Vu\u010di\u0107 ta kuma shafi ayyukan samar da ababen more rayuwa na hadin gwiwa\u00a0 a fannin makamashi, da kuma samar da isasshen abinci gabanin lokacin sanyi a Ukraine.<\/p>\n<p>Ukraine ta samu barna mai yawa a fannin ababen more rayuwar samar da makamashi sakamakon hare-haren da Rasha ta rika kaiwa akai-akai, lamarin da ya haifar da damuwa game da samar da makamashi a lokacin sanyin da ke tafe.<\/p>\n<p>Duk da goyon bayan da Serbia ke bai wa mutuncin yankunan Ukraine, Belgrade ta ci gaba da kin amincewa da sanarwar &#8216;yancin kan Kosovo da aka yi a shekarar 2008. Ukraine ita ma ba ta amince da &#8216;yancin kan Kosovo ba kuma ta ci gaba da kallonsa a matsayin wani bangare na Serbia.<\/p>\n<p>Matsayin Vu\u010di\u0107 yana nuna kokarin Serbia na kiyaye kusancin dangantaka da Rasha yayin da take ci gaba da burinta na dogon lokaci na shiga kungiyar Tarayyar Turai.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Reuters\/Aisha.Yahaya,\u00a0 Lagos<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaban kasar Serbia, Aleksandar Vu\u010di\u0107, ya bayyana a ranar Asabar cewa kasarsa ta sake jaddada goyon bayanta ga &#8216;yancin kai da kuma mutuncin yankunan kasar Ukraine, yayin da take kokarin karfafa hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu. Vu\u010di\u0107 ya bayyana hakan ne yayin ziyarar kwana biyu da shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelenskiy, ya kai &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":3,"featured_media":2703,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[40],"tags":[],"class_list":["post-2709","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-world-news"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2709","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/3"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=2709"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2709\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2713,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2709\/revisions\/2713"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/2703"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=2709"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=2709"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=2709"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}