{"id":2563,"date":"2026-08-07T08:25:19","date_gmt":"2026-08-07T08:25:19","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=2563"},"modified":"2026-08-07T08:39:34","modified_gmt":"2026-08-07T08:39:34","slug":"arsenal-ta-tsawaita-yarjejeniyar-ha%c9%97in-gwiwa-da-emirates-har-zuwa-shekarar-2033","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/08\/07\/arsenal-ta-tsawaita-yarjejeniyar-ha%c9%97in-gwiwa-da-emirates-har-zuwa-shekarar-2033\/","title":{"rendered":"Arsenal Ta Tsawaita Yarjejeniyar Ha\u0257in Gwiwa Da Emirates Har Zuwa Shekarar 2033."},"content":{"rendered":"<p><strong>Kungiyar Arsenal ta tsawaita yarjejeniyar hadin gwiwarta da kamfanin jiragen sama na Emirates har zuwa shekarar 2033, kamar yadda kungiyar ta Premier League ta sanar a ranar Alhamis; hakan na nufin kamfanin zai ci gaba da zama babban mai daukar nauyin kungiyar (ta hanyar sanya sunansa a gaban rigar &#8216;yan wasa), da kuma daukar nauyin kayan atisaye da kuma mallakar hakkin sanya sunansa a filin wasan kungiyar.<\/strong><\/p>\n<p>Ba a bayyana cikakkun bayanai game da kudaden yarjejeniyar ba.<\/p>\n<p>Wannan tsawaita yarjejeniya na ci gaba da hadin gwiwar da ta shafe shekaru 20, wadda ta fara a shekarar 2006 lokacin da Arsenal ta koma filin wasa na Emirates Stadium.<\/p>\n<p>Sabunta yarjejeniyar ya zo ne a wani muhimmin lokaci a tarihin kungiyar bayan nasarar da ta samu na lashe gasar Premier League a kakar wasan da ta gabata.<\/p>\n<p>Sabuwar yarjejeniyar za ta tabbatar da ci gaba da gudanar da shirye-shirye da dama, ciki har da gasar Emirates Cup, inda Arsenal za ta karbi bakuncin kungiyar Borussia Dortmund a gasar ta bana a ranar Lahadi da ta gabata.<\/p>\n<p><em><strong>&#8220;Lashe gasar Premier League babban abin alfahari ne a tarihin kungiyarmu, kuma nasara ce ta kowa da ke da alaka da Arsenal,&#8221;<\/strong><\/em> in ji Babban Jami&#8217;in Gudanarwa Richard Garlick a cikin wata sanarwa.<\/p>\n<p><em><strong>&#8220;Kamfanin Emirates ya taka muhimmiyar rawa wajen samun wannan nasara, inda ya tsaya tare da mu a duk tsawon wannan tafiya tare da raba lokuta masu muhimmanci, kalubale, da nasarorin da suka siffanta kungiyarmu a cikin shekaru 20 da suka gabata.&#8221;<\/strong><\/em><\/p>\n<p>Arsenal da Emirates, wadanda za su cika shekaru 20 da fara hadin gwiwarsu a mako mai zuwa, za su kuma fitar da wani gajeren fim na talla don murnar muhimman lokuta a cikin wannan dangantaka, wanda zai nuna tsohon dan wasan baya na Arsenal da Jamus, Per Mertesacker.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Aisha.Yahaya,\u00a0 Lagos<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Reuters\/Aisha.Yahaya, Lagos<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Kungiyar Arsenal ta tsawaita yarjejeniyar hadin gwiwarta da kamfanin jiragen sama na Emirates har zuwa shekarar 2033, kamar yadda kungiyar ta Premier League ta sanar a ranar Alhamis; hakan na nufin kamfanin zai ci gaba da zama babban mai daukar nauyin kungiyar (ta hanyar sanya sunansa a gaban rigar &#8216;yan wasa), da kuma daukar nauyin &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":3,"featured_media":2566,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[41],"tags":[],"class_list":["post-2563","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-sports-news"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2563","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/3"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=2563"}],"version-history":[{"count":3,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2563\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2569,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2563\/revisions\/2569"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/2566"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=2563"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=2563"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=2563"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}