{"id":2303,"date":"2026-08-03T09:45:28","date_gmt":"2026-08-03T09:45:28","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=2303"},"modified":"2026-08-03T09:45:28","modified_gmt":"2026-08-03T09:45:28","slug":"shugaba-trump-ya-tabbatar-da-tattaunawar-nukiliya-da-iran-a-ranar-litinin","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/08\/03\/shugaba-trump-ya-tabbatar-da-tattaunawar-nukiliya-da-iran-a-ranar-litinin\/","title":{"rendered":"Shugaba Trump Ya Tabbatar Da Tattaunawar Nukiliya Da Iran A Ranar Litinin."},"content":{"rendered":"<p dir=\"ltr\"><strong>Shugaban Amurka Donald Trump ya tabbatar da cewa za a fara tattaunawa da Iran a ranar Litinin yayin da ake ci gaba da kokarin kawo karshen rikici da kuma sake bude mashigar ruwa ta Strait of Hormuz, amma ya ki sanya takamaiman lokacin da za a cimma yarjejeniya.<\/strong><\/p>\n<p dir=\"ltr\">Da yake yi wa manema labarai magana a ranar Lahadi da ta gabata, bayan dawowarsa Washington, Trump ya ce za a fara tattaunawar ne da yammacin ranar Litinin amma bai bayyana wurin da za a yi ta ba ko kuma wadanda za su halarta. Lokacin da aka tambaye shi ko Iran tana da wa&#8217;adin cimma yarjejeniya, sai ya amsa da cewa: <em><strong>&#8220;Shin na fi son cimma yarjejeniya? Ba na son kashe mutane domin mutane na mutuwa, mutane da yawa na mutuwa, kuma ba ma son hakan.&#8221;<\/strong><\/em><\/p>\n<p dir=\"ltr\">Tun da farko Trump ya bayyana a shafin Truth Social cewa Iran da sauran kasashen Gabas ta Tsakiya sun nemi karin lokaci domin kammala yarjejeniyar da za ta kai ga sake bude mashigar Strait of Hormuz <em><strong>&#8220;nan take, gaba daya kuma ba tare da wani sharadi ba&#8221;<\/strong> <\/em>tare da <em><strong>&#8220;kawo karshen barazanar nukiliyar <\/strong><strong>Ira<\/strong><strong>n,&#8221;<\/strong> <\/em>yayin da ya jaddada cewa dole ne Tehran ta <em><strong>&#8220;cimma yarjejeniya cikin gaggawa.&#8221;<\/strong><\/em><\/p>\n<p dir=\"ltr\">Ana gudanar da tattaunawar ne bayan watanni na karuwar tashin hankali sakamakon ayyukan soji na Amurka da Isra&#8217;ila kan Iran. Matakin da Tehran ta dauka na rufe mashigar Strait of Hormuz\u2014inda kusan kashi 20 cikin 100 na man fetur da iskar gas na duniya ke bi\u2014ya haifar da tashin farashin makamashi, duk da cewa farashin man fetur ya fadi da fiye da kashi 4 cikin 100 a farkon cinikin ranar Litinin da ta gabata, sakamakon sabon fatan da aka samu na hanyar diflomasiyya.<\/p>\n<p dir=\"ltr\">KARANTA KUMA: Majalisar Wakilan Amurka ta Kada kuri&#8217;ar Takaita Ikon Trump na Yaki da Iran<\/p>\n<div align=\"left\">\n<p dir=\"ltr\">A halin yanzu, Iran ta kara kaimi wajen harkokin diflomasiyya, inda Ministan Harkokin Waje Abbas Araqchi ya gudanar da tattaunawa da Saudiyya da Pakistan. Jami&#8217;an Iran sun kuma tabbatar da cewa tattaunawa da Oman kan sabuwar hanyar jigilar kaya ta mashigar Strait of Hormuz na gab da kammalawa, inda suka jaddada cewa tattaunawar<em><strong> &#8220;ba ta da alaka da batun bude ko rufe mashigar Strait of Hormuz. Wannan wani batu ne daban.&#8221;<\/strong><\/em><\/p>\n<p dir=\"ltr\">Duk da kokarin diflomasiyyar, Isra&#8217;ila ta ci gaba da tsayawa kan matsayinta mai tsauri. Ministan Makamashi Eli Cohen ya yi gargadin cewa: <em><strong>&#8220;Ko an cimma yarjejeniya ko a&#8217;a, kuma ko mene ne alkawuran da aka yi daga waje, idan Iran ta yi yunkurin farfado da shirin nukiliyarta ko bunkasa masana&#8217;antun makamai masu linzami masu nisan zango, za mu dauki mataki. <\/strong><\/em><br \/>\n<em><strong>Za mu dauki mataki, kuma za mu kai hari.&#8221;<\/strong><\/em><\/p>\n<p dir=\"ltr\">Trump da Firayim Ministan Isra&#8217;ila Benjamin Netanyahu sun gana a Washington a makon da ya gabata domin tattauna hanyoyin diflomasiyya, tattalin arziki da na soja don dakile shirin nukiliyar Iran, yayin da Tehran ke ci gaba da musanta cewa tana neman mallakar makaman nukiliya.<\/p>\n<p dir=\"ltr\">\n<\/div>\n<p dir=\"ltr\">\n<p dir=\"ltr\">\n<p dir=\"ltr\">\n<div align=\"left\">\n<p dir=\"ltr\">Reuters\/Aisha.Yahaya, Lagos<\/p>\n<\/div>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaban Amurka Donald Trump ya tabbatar da cewa za a fara tattaunawa da Iran a ranar Litinin yayin da ake ci gaba da kokarin kawo karshen rikici da kuma sake bude mashigar ruwa ta Strait of Hormuz, amma ya ki sanya takamaiman lokacin da za a cimma yarjejeniya. Da yake yi wa manema labarai magana &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":3,"featured_media":2306,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[40],"tags":[],"class_list":["post-2303","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-world-news"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2303","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/3"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=2303"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2303\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2308,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2303\/revisions\/2308"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/2306"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=2303"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=2303"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=2303"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}