{"id":2078,"date":"2026-07-30T12:46:33","date_gmt":"2026-07-30T12:46:33","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=2078"},"modified":"2026-07-30T12:46:33","modified_gmt":"2026-07-30T12:46:33","slug":"ana-yi-wa-shugaban-yan-adawar-uganda-magani-a-sashen-kula-da-masu-tsananin-rashin-lafiya","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/07\/30\/ana-yi-wa-shugaban-yan-adawar-uganda-magani-a-sashen-kula-da-masu-tsananin-rashin-lafiya\/","title":{"rendered":"Ana Yi Wa Shugaban &#8216;Yan Adawar Uganda Magani A  Sashen Kula Da Masu Tsananin Rashin lafiya."},"content":{"rendered":"<p><strong>An kwantar da fitaccen jagoran &#8216;yan adawa na Uganda, Dr. Kizza Besigye, a sashin kula da masu tsananin rashin lafiya (ICU) na Asibitin Mulago National Referral da ke Kampala bayan ya fadi sumamme yayin shari&#8217;ar tuhumarsa da laifin cin amanar kasa a ranar Laraba da ta gabata; matarsa, Winnie Byanyima, ce ta bayyana hakan a ranar Alhamis da ta gabata.<\/strong><\/p>\n<p>Byanyima, wacce kuma ita ce Daraktar Zartarwa ta Shirin Majalisar Dinkin Duniya na hadin gwiwa kan cutar HIV\/AIDS (UNAIDS), ta bayyana a shafinta na X cewa dan siyasar mai shekaru 70 yana cikin halin rashin hayyacinsa kuma yanayinsa na da matukar tsanani.<\/p>\n<p>&#8220;<em><strong>Ba ya cikin hayyacinsa, ba ya iya magana, kuma ba ya nuna wata alamar jin zafi ko martani idan aka taba shi,&#8221;<\/strong><\/em> in ji ta.<\/p>\n<p>Besigye ya fadi sumamme ne yayin da yake gabatar da kansa a gaban kotu a babban birnin kasar Uganda, inda ake tuhumarsa da laifin cin amanar kasa. Nan take aka dauke shi daga zauren kotun a cikin motar daukar marasa lafiya zuwa babban asibitin kasar.<\/p>\n<p>Kakakin gwamnati Alan Kasujja bai mayar da martani ba kan bukatar jin ta bangaren gwamnati game da wannan lamari.<\/p>\n<p>KARANTA KUMA: &#8216;Yan sandan Uganda sun musanta kama jagoran &#8216;yan adawa<\/p>\n<p>Ya dade yana tsare tun watan Nuwamban 2024 bayan an kama shi da mataimakinsa, Obeid Lutale, a kasar Kenya makwabciya tare da dawo da su Uganda, inda aka tuhume su duka biyun da laifin cin amanar kasa.<\/p>\n<p>Lauyoyinsa, magoya bayansa, da kungiyoyin kare hakkin dan adam sun sha bayyana cewa tuhumar na da nasaba da siyasa, inda suke zargin cewa tsawaita tsare shi wani bangare ne na matakan murkushe &#8216;yan adawa da gwamnatin Shugaba Yoweri Museveni ke dauka.<\/p>\n<p>Besigye, wanda ya dade yana sukar Museveni, ya taba tsayawa takarar shugaban kasa sau da dama inda ya fafata da shugaban mai dadewa kan karagar mulki. Tsare shi da aka yi a wannan karon ya haifar da damuwa ga masu fafutukar kare hakkin dan adam a ciki da wajen Uganda.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Reuters\/Aisha.Yahaya, Lagos<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>An kwantar da fitaccen jagoran &#8216;yan adawa na Uganda, Dr. Kizza Besigye, a sashin kula da masu tsananin rashin lafiya (ICU) na Asibitin Mulago National Referral da ke Kampala bayan ya fadi sumamme yayin shari&#8217;ar tuhumarsa da laifin cin amanar kasa a ranar Laraba da ta gabata; matarsa, Winnie Byanyima, ce ta bayyana hakan a &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":3,"featured_media":2090,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[42],"tags":[],"class_list":["post-2078","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-afica-news"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2078","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/3"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=2078"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2078\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2091,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/2078\/revisions\/2091"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/2090"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=2078"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=2078"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=2078"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}