{"id":1995,"date":"2026-07-29T08:52:25","date_gmt":"2026-07-29T08:52:25","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=1995"},"modified":"2026-07-29T08:52:25","modified_gmt":"2026-07-29T08:52:25","slug":"sarkin-timi-na-ede-ya-yi-kira-ga-shugaba-tinubu-da-ya-tabbatar-an-gudanar-da-ingantaccen-zabe","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/07\/29\/sarkin-timi-na-ede-ya-yi-kira-ga-shugaba-tinubu-da-ya-tabbatar-an-gudanar-da-ingantaccen-zabe\/","title":{"rendered":"Sarkin Timi Na Ede Ya Yi Kira Ga Shugaba Tinubu Da Ya Tabbatar An Gudanar Da Ingantaccen Zabe."},"content":{"rendered":"<p><strong>Timi na Ede, Oba Munirudeen Adesola Lawal, ya yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya tabbatar an gudanar da zaben gwamna mai &#8216;yanci, adalci, da kuma amincewa a Jihar Osun a ranar 15 ga watan Agusta.<\/strong><\/p>\n<p>Ya bukaci Shugaban kasar da ya yi amfani da mukaminsa wajen tabbatar da daidaiton dama ga dukkan jam&#8217;iyyun siyasa, yana mai cewa dimokuradiyya tana samun ci gaba ne kawai idan an bi ra&#8217;ayin jama&#8217;a kuma &#8216;yan kasa suka samu damar zaben shugabannin da suke so ba tare da tsoratarwa ko wani cikas ba.<\/p>\n<p>Oba Lawal ya kuma yi kira da a kaddamar da aikin fadada hanyar Akoda\u2013Baptist High School\u2013Oke Gada da ke Karamar Hukumar Ede ta Kudu a Jihar Osun.<\/p>\n<p><em><strong>&#8220;Ina amfani da wannan dama wajen yin kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya tabbatar an gudanar da zaben gwamna mai &#8216;yanci, adalci, da amincewa; ya kamata ya bar mutanen Jihar Osun su zabi dan takarar da suke so a ranar 15 ga watan Agusta,&#8221;<\/strong> <\/em>in ji shi.<\/p>\n<p>Sai dai, basaraken ya bayyana cewa kofarsa a bude take ga dukkan jam&#8217;iyyun siyasa da masu neman mukamai, yayin da ya bukaci mutanen Ede su fito kwansu da kwarkwatarsu su zabi Gwamna Ademola Adeleke, yana mai cewa, <em><strong>&#8220;Za mu yi amfani da kuri&#8217;unmu wajen saka wa gwamnatin Adeleke kan manyan ayyukan ci gaba da samar da ababen more rayuwa da ta yi a garin Ede.<\/strong><\/em><\/p>\n<p><em><strong>&#8220;Haka kuma za mu yi amfani da kuri&#8217;unmu wajen cike duk wani gibin da aka samu daga sauran kananan hukumomin Jihar Osun. Za mu cike akwatunan zabe har su cika makil; Allah Ya sanya mu a matsayi mai muhimmanci da fifiko,&#8221;<\/strong> <\/em>in ji shi.<\/p>\n<p>KARANTA KUMA: Gwamnan Jihar Osun Ya Yi Alkawarin Gudanar da Zabe Mai Inganci a ranar 15 ga Agusta<\/p>\n<p><strong>An Cika Alkawari \u2013 Gwamna<\/strong><\/p>\n<p>Yayin da yake jawabi ga jama&#8217;a a wajen kaddamar da aikin, Gwamna Adeleke ya bayyana cewa hanyar <em><strong>&#8220;alkawari ne da aka cika shi,&#8221;<\/strong> <\/em>yana mai jaddada cewa za ta hanzarta ci gaban tsohon garin na Ede.<\/p>\n<p><em><strong>&#8220;Wannan alkawari ne da aka cika, kuma wannan shi ne irin shugabancin da ke shafar zukatan jama&#8217;a. Wannan hanya tana da matukar muhimmanci ga Ede; tana hada manyan unguwannin zama, makarantu, da kasuwa, tare da hada su da hanyoyin da ke zuwa manyan biranen Osogbo da Ibadan. \u201c<\/strong><\/em>Tsawon lokaci, al\u2019ummarmu sun sha fama da cunkoson ababen hawa da kuma rashin ingantattun hanyoyi a cikin garin. Sai dai tare da wannan hanyar mai layuka biyu, zirga-zirga a cikin Ede za ta kasance cikin sauri da kwanciyar hankali; harkokin kasuwanci a yankunan Akoda, Cottage, da Oke Gada za su bunkasa; dalibai da ma\u2019aikata za su rika isa makarantu da wuraren aikinsu akan lokaci; sannan harkokin dare da tsaro za su inganta sakamakon samar da fitilun hasken rana.<\/p>\n<p><em><strong>\u201cWannan wani bangare ne na tsarin gwamnatinmu na farfado da kayayyakin more rayuwa a dukkan yankunan jihar Osun. Abin da muke yi a Osogbo, shi muke yi a Ila, Iwo, Ile Ife, Ilesha, kuma yanzu a Ede,\u201d<\/strong> <\/em>in ji Gwamnan.<\/p>\n<p>Gwamnan ya yabawa ma\u2019aikatar ayyuka da kuma \u2018yan kwangilar da suka yi aiki mai kyau, inda ya ce injiniyoyin sun yi aiki mai inganci daidai gwargwado.<\/p>\n<p>Yayin da yake kaddamar da titin biyu a hukumance, Adeleke ya bayyana fatan cewa jam&#8217;iyyar Accord Party za ta yi nasara a zaben.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Aisha.Yahaya, Lagos<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Timi na Ede, Oba Munirudeen Adesola Lawal, ya yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya tabbatar an gudanar da zaben gwamna mai &#8216;yanci, adalci, da kuma amincewa a Jihar Osun a ranar 15 ga watan Agusta. Ya bukaci Shugaban kasar da ya yi amfani da mukaminsa wajen tabbatar da daidaiton dama ga dukkan jam&#8217;iyyun &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":3,"featured_media":1999,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[39],"tags":[],"class_list":["post-1995","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-nigeria-news"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1995","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/3"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=1995"}],"version-history":[{"count":3,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1995\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":2002,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1995\/revisions\/2002"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/1999"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=1995"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=1995"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=1995"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}