{"id":1912,"date":"2026-07-27T12:13:34","date_gmt":"2026-07-27T12:13:34","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=1912"},"modified":"2026-07-27T12:13:34","modified_gmt":"2026-07-27T12:13:34","slug":"shugaba-tinubu-ya-nada-olanrewaju-smart-a-matsayin-mai-ba-da-shawara-na-musamman","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/07\/27\/shugaba-tinubu-ya-nada-olanrewaju-smart-a-matsayin-mai-ba-da-shawara-na-musamman\/","title":{"rendered":"Shugaba Tinubu Ya Nada Olanrewaju Smart A Matsayin Mai Ba Da Shawara Na Musamman."},"content":{"rendered":"<p><strong>Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada Dr. Wasiu Olanrewaju-Smart a matsayin Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Majalisar Dokoki ta Kasa, musamman bangaren Majalisar Wakilai.<\/strong><\/p>\n<p>A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban Kasa, Bayo Onanuga, ya fitar, an bayyana cewa Dr. Olanrewaju-Smart zai maye gurbin Ibrahim Olanrewaju, wanda ya yi murabus daga mukaminsa domin neman takarar wani mukami a jiharsa ta asali.<\/p>\n<p>Olanrewaju-Smart kwararren masani ne a fannin tsare-tsaren gwamnati (public policy). Yana da digirin digirgir (PhD) a fannin Gudanarwar Ilimi daga Jami&#8217;ar Lead City da kuma digiri na biyu (Master\u2019s) a fannin Gudanarwar Jama&#8217;a daga Jami&#8217;ar Harvard.<\/p>\n<p>A halin yanzu, yana aiki a matsayin &#8216;Edward Mason Fellow&#8217; a fannin tsare-tsaren gwamnati a Harvard Kennedy School. Wannan kwararre kan tsare-tsare, mai shekaru 40, ya taba rike mukamin &#8216;<strong>LEAPS Fellow&#8217;<\/strong> a Cibiyar Fasaha ta Massachusetts (<strong>MIT),<\/strong> sannan yana da takardar shedar kwarewa ta musamman a fannin Hulda da Jama&#8217;a (Public Relations) daga London School of Public Relations.<\/p>\n<p>KARANTA KUMA: Shugaba Tinubu zai halarci Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya na shekarar 2026<\/p>\n<p>Bugu da kari, ya yi aiki a matsayin &#8216;<strong>Policy Fellow&#8217;<\/strong> a kamfanin Quantum Alliance AI da ke Amurka, inda ya mayar da hankali kan hadewar fasahar basirar dan-adam (AI) da fasahar da ke amfanar al&#8217;umma (civic technology).<\/p>\n<p>Ayyukansa a Majalisar Dokoki ta Kasa sun hada da mukamai daban-daban, tun daga Mataimaki kan Bincike da Yada Labarai ga Shugabannin &#8216;Yan Tsiraru da &#8216;Yan Rinjaye na Majalisar Wakilai a zaman majalisa na 7 da na 8, har zuwa mukaman Mataimaki na Musamman, Mataimakin Shugaban Ma&#8217;aikata, da kuma Shugaban Ma&#8217;aikata ga Kakakin Majalisar Wakilai a zaman majalisa na 9 da na 10.<\/p>\n<p>Daga baya, Olanrewaju-Smart ya shiga fadar shugaban kasa a watan Oktoban 2023, a matsayin Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Hadin Gwiwar Gwamnatoci (Intergovernmental Affairs), mukamin da ya rike har zuwa lokacin da aka yi wannan sabon nadin.<\/p>\n<p>Ayyukansa na bincike kan tsare-tsaren gwamnati sun hada da gudummawa wajen samar da muhimman dokoki, kamar Dokar Lamunin Karatu mara Ruwa (Interest-Free Student Loan Act), da sauransu.<\/p>\n<p>Shugaba Tinubu ya nuna kwarin gwiwar cewa Olanrewaju-Smart zai yi amfani da gogewarsa, hazakarsa, da kuma kwazonsa wajen inganta hadin gwiwar majalisa da kuma karfafa alaka mai amfani tsakanin Fadar Shugaban Kasa, Ma&#8217;aikatu, Sassan Gwamnati, da Hukumomi (MDAs) da kuma Majalisar Wakilai.<\/p>\n<p>Wannan nadi ya fara aiki nan take.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Aisha.Yahaya, Lagos<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada Dr. Wasiu Olanrewaju-Smart a matsayin Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Majalisar Dokoki ta Kasa, musamman bangaren Majalisar Wakilai. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban Kasa, Bayo Onanuga, ya fitar, an bayyana cewa Dr. Olanrewaju-Smart zai maye gurbin Ibrahim Olanrewaju, wanda ya yi &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":3,"featured_media":1915,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[39],"tags":[],"class_list":["post-1912","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-nigeria-news"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1912","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/3"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=1912"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1912\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":1917,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1912\/revisions\/1917"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/1915"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=1912"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=1912"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=1912"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}