{"id":1756,"date":"2026-07-23T17:08:46","date_gmt":"2026-07-23T17:08:46","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=1756"},"modified":"2026-07-23T17:08:46","modified_gmt":"2026-07-23T17:08:46","slug":"masar-ta-mamaye-gasar-zakarun-matasa-ta-ittf-a-afirka","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/07\/23\/masar-ta-mamaye-gasar-zakarun-matasa-ta-ittf-a-afirka\/","title":{"rendered":"Masar Ta Mamaye Gasar Zakarun Matasa Ta ITTF A Afirka"},"content":{"rendered":"<p><strong>Masar ta lashe kofuna uku cikin hudu na gasar kungiyoyi a gasar matasa ta ITTF ta Afirka ta shekarar 2026, lamarin da ya sake tabbatar da karfinta da kuma yadda ta ke kan gaba a wasan kwallon tebur na matasa a nahiyar Afirka.<\/strong><\/p>\n<p>An buga wasannin karshe a ranar Laraba a cibiyar wasanni ta Borteyman da ke Accra, Ghana.<\/p>\n<p>Kasar ta Arewacin Afirka ta doke Najeriya, Tunisia, da Algeria domin lashe kofunan matasa &#8216;yan kasa da shekaru 15 (npjja maza da mata), tare da ci gaba da rike kambun &#8216;yan kasa da shekaru 19 na mata.<\/p>\n<p>Najeriya, wacce ta zo gasar a matsayin wacce ta lashe kofin a baya, ta fuskanci kalubale mai tsanani kafin ta samu nasara kan kasar da ta karbi bakuncin gasar, wato Ghana, da ci 3-2 a matakin kusa da na karshe.<\/p>\n<p>Sai dai, Masar ta nuna karfi sosai a wasan karshe, inda ta doke Najeriya da ci 3-0 ba tare da ko daya ba.<\/p>\n<p>Ahmed Elsabbagh ne ya fara bude asusun cin kwallaye ta hanyar doke Marvelous Joseph da ci 3-0 (maki 11-8, 11-5, 13-11).<\/p>\n<p>Daga nan, babban dan wasan Masar, Asser Sameh, ya doke Usman Ayoola da ci 3-0 (maki 11-9, 12-10, 11-7).<\/p>\n<p>Hussein Eyad ya kammala nasarar da babbar kwazo ta hanyar doke Samson Joshua da ci 3-0 (maki 11-9, 11-9, 11-8).<\/p>\n<p>Karanta kuma: Masar, Najeriya, da Tunisia Sun Fara Gasar Matasa ta ITTF da Karfi<\/p>\n<p>ITTF na Karfafa Gwiwar Kasashen Afirka su Nemi Karbar Bakuncin Gasar Bayan Nasarar da aka samu a Ghana<\/p>\n<p>A bangaren &#8216;yan kasa da shekaru 15 na mata, Masar ta doke Tunisia da ci 3-1 domin kwato kambun da ta rasa a hannun Uganda a shekarar 2025.<\/p>\n<p>Har ila yau, &#8216;yan wasan Masar sun ci gaba da rike kambun &#8216;yan kasa da shekaru 19 na mata bayan sun doke Algeria da ci 3-0.<\/p>\n<p>Kasancewar ta lashe kofuna uku na kungiyoyi, nasarar da Masar ta samu a Accra ta kara tabbatar da karfinta da kuma yadda ta ke ci gaba da mamaye wasan kwallon tebur na matasa a Afirka.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>NAN\/Aisha.Yahaya, Lagos<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Masar ta lashe kofuna uku cikin hudu na gasar kungiyoyi a gasar matasa ta ITTF ta Afirka ta shekarar 2026, lamarin da ya sake tabbatar da karfinta da kuma yadda ta ke kan gaba a wasan kwallon tebur na matasa a nahiyar Afirka. An buga wasannin karshe a ranar Laraba a cibiyar wasanni ta Borteyman &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":3,"featured_media":1759,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[41],"tags":[],"class_list":["post-1756","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-sports-news"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1756","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/3"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=1756"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1756\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":1761,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1756\/revisions\/1761"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/1759"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=1756"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=1756"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=1756"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}