{"id":1695,"date":"2026-07-22T09:41:46","date_gmt":"2026-07-22T09:41:46","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=1695"},"modified":"2026-07-22T09:41:46","modified_gmt":"2026-07-22T09:41:46","slug":"shugaba-tinubu-ya-taya-sabon-firayim-ministan-birtaniya-murna","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/07\/22\/shugaba-tinubu-ya-taya-sabon-firayim-ministan-birtaniya-murna\/","title":{"rendered":"Shugaba Tinubu Ya Taya Sabon Firayim Ministan Birtaniya Murna."},"content":{"rendered":"<p>&nbsp;<\/p>\n<p><strong>Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya taya Andy Burnham murna bisa kar\u0253ar ragamar mulki a matsayin Firayim Ministan Birtaniya.<\/strong><\/p>\n<p>Shugaban ya sake nanata kudirin Najeriya na karfafa dangantakar dabarun hadin gwiwa da Birtaniya.<\/p>\n<p>A cikin wata sanarwa da kakakin ma&#8217;aikatar harkokin waje, Kimiebi Ebienfa, ya fitar, Shugaba Tinubu ya kuma taya gwamnati da al&#8217;ummar Birtaniya murna kan abin da ya kira mika mulki cikin lumana, tsari, da sauki, yana mai cewa hakan ya nuna karfin cibiyoyin dimokradiyya da al&#8217;adun tsarin mulkin kasar.<\/p>\n<p>Shugaban ya tuna ziyarar aiki da ya kai Birtaniya a watan Maris na 2026, inda ya gudanar da tattaunawa mai amfani da Firayim Ministan da ya gabata.<\/p>\n<p>KARANTA KUMA: Shugaba Tinubu ya taya Badejo-Okusanya murna kan nasarar zaben NBA<\/p>\n<p>Ya bayyana kwarin gwiwar cewa Firayim Minista Burnham zai ci gaba da gina harsashin nasarorin da aka samu a waccan tattaunawa tare da samar da sabbin damammakin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.<\/p>\n<p><em><strong>&#8220;Ina fatan binciko sabbin hanyoyin hadin gwiwa da tattaunawa tare da Birtaniya a karkashin sabon Firayim Minista,&#8221;<\/strong><\/em> in ji Shugaba Tinubu.<\/p>\n<p>Shugaban ya kuma bayyana sha&#8217;awarsa ta ganawa da Firayim Minista Burnham da wuri-wuri, ko dai a matakin kasashen biyu ko kuma a tarukan kasa da kasa, musamman a kungiyar Commonwealth, domin zurfafa dangantaka da kuma ciyar da muradun gama-gari gaba.<\/p>\n<p>Ya sake nanata shirye-shiryen Najeriya na yin aiki kafada-da-kafada da sabuwar gwamnatin Birtaniya wajen inganta ci gaban juna da kuma tunkarar kalubalen duniya da ya shafi kowa.<\/p>\n<p>Shugaba Tinubu ya yi wa Firayim Minista Burnham fatan samun nasara a wa&#8217;adin mulkinsa tare da tabbatar masa da ci gaba da kudirin Najeriya na karfafa dangantaka mai dorewa tsakanin kasashen biyu.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Aisha.Yahaya, Lagos<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>&nbsp; Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya taya Andy Burnham murna bisa kar\u0253ar ragamar mulki a matsayin Firayim Ministan Birtaniya. Shugaban ya sake nanata kudirin Najeriya na karfafa dangantakar dabarun hadin gwiwa da Birtaniya. A cikin wata sanarwa da kakakin ma&#8217;aikatar harkokin waje, Kimiebi Ebienfa, ya fitar, Shugaba Tinubu ya kuma taya gwamnati da al&#8217;ummar Birtaniya &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":3,"featured_media":1698,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[39],"tags":[],"class_list":["post-1695","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-nigeria-news"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1695","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/3"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=1695"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1695\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":1700,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1695\/revisions\/1700"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/1698"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=1695"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=1695"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=1695"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}