{"id":1680,"date":"2026-07-22T09:08:57","date_gmt":"2026-07-22T09:08:57","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=1680"},"modified":"2026-07-22T09:08:57","modified_gmt":"2026-07-22T09:08:57","slug":"jamiyyar-labour-sun-aamince-da-okereke-da-konto-a-2027","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/07\/22\/jamiyyar-labour-sun-aamince-da-okereke-da-konto-a-2027\/","title":{"rendered":"Jam&#8217;iyyar Labour Sun Aamince Da Okereke Da Konto A 2027"},"content":{"rendered":"<p><strong>Shugabancin jam&#8217;iyyar Labour Party na kasa a Najeriya ya sake jaddada amincewarsa ga dan takarar shugaban kasa na jam&#8217;iyyar a zaben 2027, Dr. Chibuzo Okereke, da kuma takwararsa mai neman mataimakin shugaban kasa, Hajia Konto, gabanin babban zaben 2027.<\/strong><\/p>\n<p>An bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa da aka gudanar tare da dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam&#8217;iyyar, Hajia Bintu Konto, a hedikwatar jam&#8217;iyyar ta kasa da ke Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.<\/p>\n<p>Da take jawabi a wajen taron, Shugaban jam&#8217;iyyar Labour Party ta kasa, Sanata Nenadi Usman, ta bayyana gamsuwarta matuka game da zabar Hajia Bintu Konto a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam&#8217;iyyar, inda ta bayyana zabin a matsayin <strong><em>&#8220;madubin jajircewar jam&#8217;iyyar Labour Party wajen tabbatar da daidaito, hada kowa da kowa, da kuma adalci a zamantakewa.&#8221;<\/em><\/strong><\/p>\n<p>A cewar Usman, <em><strong>&#8220;zabar Hajia Konto ya yi daidai da falsafar jam&#8217;iyyar mai dorewa ta &#8216;Mama, Papa, Pikin&#8217; (Uwa, Uba, Da), wadda ke kunshe da halayen jin kai da manufofin jam&#8217;iyyar na hada kowa da kowa.&#8221;<\/strong><\/em><\/p>\n<p>A cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na jam&#8217;iyyar na kasa, Mista Ken Asugwa, ya fitar, Shugabar jam&#8217;iyyar ta kasa ta bayyana cewa ta hanyar tsayar da mace a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa, <em><strong>&#8220;jam&#8217;iyyar Labour Party ta sake nuna cikakken imaninta ga samar da dama mai daidai da kuma adalci a zamantakewa.&#8221;<\/strong><\/em><\/p>\n<p><em><strong>&#8220;Ta zama ita kadai ce babbar jam&#8217;iyyar siyasa a takarar shugaban kasa ta 2027 da ta bai wa mata irin wannan muhimmiyar matsayi a cikin jerin &#8216;yan takararta na shugaban kasa,&#8221;<\/strong> <\/em>in ji ta.<\/p>\n<p>Shugabar jam&#8217;iyyar ta kasa ta bayyana kwarin gwiwarta cewa cancantar Hajia Konto, da nasarorin da ta samu a fannin aikinta, da kuma gogewarta ta ayyukan jin kai za su inganta harkokin shugabanci sosai.<\/p>\n<p>Haka kuma, Sanata Usman ta yi amfani da damar wajen yaba wa salon shugabanci na misali da Gwamnan Jihar Abia, Dr. Alex Otti, ke yi, wanda ta bayyana a matsayin fuskar jam&#8217;iyyar Labour Party da kuma babban misali na shugabanci na dimokradiyya a Najeriya.<\/p>\n<p>KARANTA KUMA: Jam&#8217;iyyar Labour ta bai wa Otti fom din takarar gwamna kyauta<\/p>\n<p>Ta yaba musamman da dokar jin dadin jama&#8217;a da aka kafa kwanan nan a Jihar Abia domin tallafawa tsofaffi, inda ta bayyana hakan a matsayin misali na zahiri na gwamnatin da ta sa jama&#8217;a a gaba.<\/p>\n<p>Ta yi kira ga &#8216;yan Najeriya da jihohin da ke son ganin irin wadannan amfanin dimokuradiyya da su rungumi Jam&#8217;iyyar Labour tare da zaben ta a zabukan gaba, tana mai nuni da cewa sauye-sauyen da ke faruwa a Jihar Abia shaida ce ta zahiri kan abin da gwamnatocin Jam&#8217;iyyar Labour za su iya samarwa.<\/p>\n<p>A nasa bangaren, dan takarar shugaban kasa na jam&#8217;iyyar, Dr. Chibuzo Sunday Okereke, ya bayyana farin cikinsa da hada shi a matsayin abokin takara tare da Hajia Bintu Konto, wacce ya kwatanta a matsayin mutum mai tawali&#8217;u, amintacciya, kuma gogaggiyar abokiyar aiki.<\/p>\n<p>Yayin da yake yaba wa Jam&#8217;iyyar Labour bisa fahimtar muhimmiyar rawar da mata ke takawa wajen gina kasa, Dr. Okereke ya bayyana cewa yin watsi da mata a harkokin mulki tamkar yunkurin tafa hannu daya ne kawai, musamman idan aka yi la&#8217;akari da gagarumar gudunmawar da suke bayarwa ga yawan al&#8217;ummar Najeriya da ci gaban kasa.<\/p>\n<p>Ya yaba matuka da tarihin Hajia Konto a matsayinta na fitacciyar mai fafutukar ci gaba da kuma kwararriya a fannin kiwon lafiyar jama&#8217;a, wacce ayyukanta suka yi tasiri mai kyau ga rayuwar mutane da dama a fadin kasar nan.<\/p>\n<p>A cewarsa, shugabancinsa ba zai cika ba sai tare da Hajia Konto a matsayin mataimakiyar shugaban kasa, kamar yadda ya ce Najeriya za ta ci gajiyar hadin gwiwar gogewarsu, kwarewarsu, da kuma manufarsu ta bai daya ta farfado da kasar.<\/p>\n<p>Dr. Okereke ya kuma yaba wa Sanata Nenadi Usman bisa jagorancinta da kuma muhimmiyar rawar da ta taka wajen fitowar Hajia Konto, inda ya kwatanta Shugabar Jam&#8217;iyyar ta kasa a matsayin shugaba abin koyi da kuma tushen karfafa gwiwa ga mata a fadin kasar nan.<\/p>\n<p>A jawabinta, &#8216;yar takarar mataimakiyar shugaban kasa, Hajia Bintu Konto, ta bayyana matukar godiyarta ga shugabanci da mambobin Jam&#8217;iyyar Labour bisa amincewar da suka nuna mata. Ta kwatanta Sanata Nenadi Usman a matsayin mace mai zuciyar zinare, wacce jajircewarta wajen tabbatar da adalmi, da daidaito, da kuma hidimtawa kasa ke ci gaba da karfafa gwiwar &#8216;yan Najeriya da dama.<\/p>\n<p>Hajia Konto ta yi alkawarin sadaukar da kanta gaba daya wajen hidimtawa kasa idan aka zabe ta a matsayin mataimakiyar shugaban kasa a shekarar 2027.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Aisha.Yahaya, Lagos<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>Shugabancin jam&#8217;iyyar Labour Party na kasa a Najeriya ya sake jaddada amincewarsa ga dan takarar shugaban kasa na jam&#8217;iyyar a zaben 2027, Dr. Chibuzo Okereke, da kuma takwararsa mai neman mataimakin shugaban kasa, Hajia Konto, gabanin babban zaben 2027. An bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa da aka gudanar tare da dan takarar mataimakin &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":3,"featured_media":1683,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[39,47],"tags":[],"class_list":["post-1680","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-nigeria-news","category-politics"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1680","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/3"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=1680"}],"version-history":[{"count":2,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1680\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":1685,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1680\/revisions\/1685"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/1683"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=1680"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=1680"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=1680"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}