{"id":1624,"date":"2026-07-21T09:45:53","date_gmt":"2026-07-21T09:45:53","guid":{"rendered":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/?p=1624"},"modified":"2026-07-21T09:45:53","modified_gmt":"2026-07-21T09:45:53","slug":"shugaban-maaikata-fadar-gwamnati-ya-amsa-gayyatar-icpc","status":"publish","type":"post","link":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/2026\/07\/21\/shugaban-maaikata-fadar-gwamnati-ya-amsa-gayyatar-icpc\/","title":{"rendered":"Shugaban Ma&#8217;aikata Fadar Gwamnati Ya Amsa Gayyatar ICPC"},"content":{"rendered":"<p><strong>A ranar Litinin da ta gabata ne Shugaban Ma&#8217;aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila, ya amsa gayyatar Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuka Masu Nasaba da Hakan (ICPC), inda ya bayyana a gaban hukumar domin amsa tambayoyi game da binciken da take gudanarwa kan ayyukan wata kungiya mai suna &#8216;Presidential Foreign Investment Promotion Council&#8217; (PFIPC) da ake ta ce-ce-ku-ce a kanta.<\/strong><\/p>\n<p>Lauyansa, Jiti Ogunye, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, inda ya yi bayanin cewa bayyanar Gbajabiamila a gaban hukumar ta zo ne bisa umarnin Shugaba Bola Tinubu.<\/p>\n<p>A cewar sanarwar, Shugaban Ma&#8217;aikatan ya isa hedikwatar ICPC da misalin karfe 3:00 na yammacin ranar Litinin da ta gabata inda ya bayar da bayanai tare da amsa tambayoyi game da binciken da ake yi kan wannan kungiya da ake zargin ta kasance ta bogi ce.<\/p>\n<p>KARANTA KUMA: Rikicin PFIPC na bukatar gyara a tsarin hukumomi da kuma bincike na gaskiya \u2014 Mataimakin Shugaban Kasa<\/p>\n<p>Ogunye ya ce <em><strong>&#8220;Cikin cikakken hadin kai da hukumar ICPC, kuma bisa umarnin Shugaban Najeriya, ina tabbatar da cewa wanda nake wakilta, Femi Gbajabiamila, wato Shugaban Ma&#8217;aikatan Fadar Shugaban Kasa, ya amsa gayyatar hukumar ICPC kuma ya bayyana a wurinta da misalin karfe 3:00 na yammacin ranar Litinin a matsayin wani bangare na binciken da ake gudanarwa kan ayyukan kungiyar PFIPC ta bogi, da sauran batutuwa.&#8221;<\/strong><\/em><\/p>\n<p>Ya kara da cewa bayan ya bayar da bayanansa tare da amsa tambayoyin hukumar, Gbajabiamila ya koma bakin aikinsa na hukuma.<\/p>\n<p>Binciken ya mayar da hankali ne kan kungiyar da ake kira &#8216;Presidential Foreign Investment Promotion Council&#8217; (PFIPC), wadda hukumomin gwamnati masu ruwa da tsaki suka musanta kasancewarta kungiya ta gwamnati, inda suka bayyana ta a matsayin kungiyar bogi da ba ta da izini kuma ba ta wanzu a hukumance.<\/p>\n<p>Gwamnatin Najeriya ta nanata cewa ba a taba kafa wannan kungiya ta hanyar da ta dace da doka ba, kuma ta yi gargadi ga jama&#8217;a game da mu&#8217;amala da ita, inda ta bayyana ta a matsayin kungiyar bogi da ke gudanar da ayyukanta a wajen tsarin gwamnati na yau da kullum.<\/p>\n<p>&nbsp;<\/p>\n<p>Aisha.Yahaya, Lagos<\/p>\n","protected":false},"excerpt":{"rendered":"<p>A ranar Litinin da ta gabata ne Shugaban Ma&#8217;aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila, ya amsa gayyatar Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuka Masu Nasaba da Hakan (ICPC), inda ya bayyana a gaban hukumar domin amsa tambayoyi game da binciken da take gudanarwa kan ayyukan wata kungiya mai suna &#8216;Presidential Foreign &hellip;<\/p>\n","protected":false},"author":3,"featured_media":1627,"comment_status":"open","ping_status":"open","sticky":false,"template":"","format":"standard","meta":{"footnotes":""},"categories":[39],"tags":[],"class_list":["post-1624","post","type-post","status-publish","format-standard","has-post-thumbnail","hentry","category-nigeria-news"],"_links":{"self":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1624","targetHints":{"allow":["GET"]}}],"collection":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts"}],"about":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/types\/post"}],"author":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/users\/3"}],"replies":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/comments?post=1624"}],"version-history":[{"count":1,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1624\/revisions"}],"predecessor-version":[{"id":1628,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/posts\/1624\/revisions\/1628"}],"wp:featuredmedia":[{"embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media\/1627"}],"wp:attachment":[{"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/media?parent=1624"}],"wp:term":[{"taxonomy":"category","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/categories?post=1624"},{"taxonomy":"post_tag","embeddable":true,"href":"https:\/\/vonlanguages.ng\/hausa\/wp-json\/wp\/v2\/tags?post=1624"}],"curies":[{"name":"wp","href":"https:\/\/api.w.org\/{rel}","templated":true}]}}